27 Faburairu 2022 - 15:04
Iran : Batutuwan Da Su Ka Rage A Teburin Tattaunawar Vienna Za A Iya Warware Su

A jiya Asabar ne ministan harkokin wajen Iran Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa; Abubuwan da su ka saura a tattaunawa da manayan kasashe biyar na duniya za a iya magance su idan har kasashen na yamma suka dauki matakan da su ka dace.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da jami’in harkokin wajen na tarayyar turai Josep Borrell.

Babban jami’in diplomasiyar na Iran ya kore jita-jitar da ake yi akan cewa Amurka ta bai wa Iran wa’adi akan ta fitar da matsaya akan tattaunawar.

Abdullahiyan ya kore jita-jitar da cewa ba ta da wani tushe.

342/